An bukaci ma'aikatan mai su kaurace wa Fort McMurray

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kusan mutum 12,000 ne aka bukace su da kaurace wa sansanonin da ke kusa da wajen da ake hako man fetur, wanda ke garin nan na Fort McMurray, domin guje wa gobarar da ake zaton na tunkarar su.

Wani jami'i a yankin ya shaida wa BBC cewa an gargadi mutum 8,000 tun daren ranar Litinin, sannan aka shawarci wasu mutum 4,000 da su kama gaban su.

Fiye da mutum 80,000 ne suka tsere bayan gobarar da ta afka wa garin Fort McMurray, makwanni biyu da suka gabata.

An shiga wani mummunan yanayi, inda iskar gurbata muhalli ta mamaye garin baki daya.

Wasu alkaluma sun nuna cewa iskar ta kai kimanin 38, wanda hakan ya zarta yadda ake bukata.

Mummunar gobarar dai ta tsagaita a Fort McMurray, amma a 'yan kwanakin nan kuma gobarar ta soma barazana a yankin kuma.