'Yar Afirka ta kudu ta dage da neman aiki

Wata 'yar Afirka ta kudu ta dage da neman aiki ta hanyar tallata wannan buƙata a jikin kwali da ta riƙe a bakin titi.

Ita dai Anthea Malwandla ta ce, ta kwashe shekara guda tana neman aiki, amma lamarin ya faskara.

Tana da digiri a fannin injiya na fasahar sanadarai daga jami'ar Vaal University of Technology.

A jikin kwalin ta ce, a taimake ta da aikin yi, kuma a shirye take da bada dukkan bayanai da ake buƙata.

Ta faɗawa BBC cewa, duk da yadda aka yaɗa ta a Twitter har yanzu ba ta yi dace da samun aiki ba.

A Afirka ta kudu alkaluma da aka fitar cikin makon jiya sun nuna cewa, rashin aikin yi ya yi ƙaruwar da ba a taɓa ganin irinta ba cikin shekaru 12.