An ba hammata iska a majalisar Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jami'an tsaro sun janye 'yan adawa daga harabar majalisar, domin sun nemi hana shugaban kasar Jacob Zuma yin jawabi.

A ranar Talata ne fada ya barke a Majalisar dokokin Afrika Ta Kudu, inda ta kai har sai da jami'an tsaro suka yi amfani da karfi wajen janye wasu 'yan majalisun da ke jam'iyyar adawa.

Lamarin ya kai wasu sun rika naushin juna a majalisar, kafin a fitar da jami'an jam'iyya mai sassauci ta Economic Freedom Fighters (watau EFF), bayan sun nemi katse jawabin shugaban kasar Jacob Zuma.

A watan Maris ne wata kotu ta yanke hukuncin cewa Mr Zuma ya keta dokokin kundin tsarin mulkin kasa, bayan da ya gaza mayar da kudaden gwamnati da ya yi amfani da su wajen yin kwaskwarima ga wani katafaren gida, mallakinsa.

Wannan dai shi ne karo na biyu da fada ya kaure a majalisar dokokin cikin wannan wata.