Shafin twitter zai daina lissafa hotuna da mashigar shafi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A baya dai hoto kadai kan ci gurbin haruffa 23

Shafin twitter zai daina lissafa hotuna da mashigar shafi wajen kayyade yawan haruffa ga masu wallafe-wallafe a shafin.

Kamfanin dillancin labarai na Bloomberg na ba da wannan labarin.

Bloomberg ya ambato majiyarsa na cewa tsarin zai fara aiki ne nan da makwanni biyu masu zuwa.

Sai dai kamfanin a nasa bangaren bai komai a kan wannan batun ba.

A watan Janairun da ya wuce ne mai shafin, Jack Dorsey ya ce twitter na duba hanyoyin ba wa ma'abota shafin damar yin wallafe-wallafe masu tsawo.

A halin da ake ciki dai mashigar shafi kadai kan ci gurbin haruffa akalla 23 daga cikin adadin 140 da aka kayyade wa kawace wallafa.

Sai dai Jack Dorsey ya ce kayyade haruffan na da ranarsa saboda yana kaifafa basirar takaita bayanai.

Amma kamfani ya gamu da kwanciyar, kasancewar ya gaza jan hankalin sabbin masu mu'amala da shafin, kuma farashinsa ya fadi da sama da kashi 70%.