An zargi yaro da kashe iyayensa a Potiskum

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan sanda sun ce matashin ya sha tramol ne.

Rundunar 'yan sandan jihar Yobe da ke arewacin Najeriya ta ce wani matashi ya yanka iyaye da ƙannensa biyu.

Kakakin rundunar, Mataimakin Sufuritanda Toyin Joshua da wasu mazauna birnin, wadanda suka tattabar wa BBC da aukuwar lamarin, sun ce matashin, mai suna Adamu Magaji Abdullahi, ya kashe mahaifinsa, Malam Abdullahi da mahaifiyarsa Hafsa da kuma ƙannensa mata biyu, Zainab da Aisha ranar Litinin da daddare.

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa matashin ya kashe mutanen ne ta hanyar amfani da shebir, kuma binciken farko ya nuna cewa ya sha ƙwayar Tramol ne.

A cewarsa, tuni aka binne mutanen da matashin ya kashe, sannan za a gurfanar da shi a gaban ƙuliya da zarar an kammala bincike.