Nigeria: Kotu ta hana PDP taro

Hakkin mallakar hoto Modu Sheriff Twitter
Image caption Ali Modu Shareef, shugaban jam'iyyar PDP a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa wata babbar kotu a birnin Legas ta hana jam'iyyar adawa ta PDP yin babban taron da ta shirya yi, a Abuja, babban birnin kasar, ranar Asabar.

Shugaban jam'iyyar na rikon kwarya, Ali Modu Shareef ne dai da sakataren jam'iyyar na kasa, Adewale Oladipo da mai binciken kudin jam'iyyar, Fatai Adeyanju suka shigar da karar neman a tsayar da taron.

Mutanen uku dai sun nemi a tsayar da taron bisa dalilin cewa wa'adinsu na shugabancin jam'iyyar bai kare ba.

Takardar karar ta kuma nemi kotun da ta hana hukumar zabe ta INEC zuwa wurin taron domin sanya ido.

Sai dai kuma an ce shugaban jam'iyyar, Ali Modu Shareef ya musanta shigar da karar.