Kamfanin Dangote ya dakatar da aiki

Image caption Ana fama da karanci da tsadar tumatir a Najeriya

Sabon kamfanin sarrafa tumatir na Dangote ya dakatar da ayyukansa sakamakon rashin samun danyen tumatur daga gona.

Mafi yawan gonakin tumatur da ke jihohin Kano da Jigawa da Filato da Katsina da kuma Kaduna sun hadu da annobar wasu kwari, wanda hakan ya yi sanadin kashe dukkan tumatirin da ke gonakin.

Wannan al'amari ya jawo wa manoma mummunar asara, da karancin tumatir da kuma tsananin tsadar dan ragowar tumatir din da ya saura a hannun manoman.

A farkon wannan shekarar ne kamfanin tumatir na Dangote da ke garin Kadawa a jihar Kano ya fara aiki.

Karin bayani