Fari: Za a tallafa wa kudancin Afrika da $110m

Kungiyoyin agaji na duniya Red Cross da Red Crescent, sun bukaci tallafin dala miliyan 110 domin kai dauki ga kasashen da ke kudancin nahiyar Afrika wadanda ke fama da fari.

An yi kiyasin cewa mutane miliyan 31.6 ne a yankin ke fuskantar matsalar karancin abinci sakamakon rashin isasshen ruwan sama, hade kuma da matsanancin karancin ruwan sha.

An gabatar da wannan bukata ne kafin taron da za a gudanar na Majalisar Dinkin Duniya, wanda zai haskaka hanyoyin da za a kafa domin kare al'umma daga matsalolin da ke da alaka da sauyin yanayi.

A kwanan baya an samu dubban mutane da suka rasa rayukansu a yankunan kudancin Afrikar, sakamakon matsanancin fari.