Trump na son ganawa da Kim Jong-un

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Trump ya ce babu wata matsala idan ya tattauna da Kim Jong-un.

Mutumin da zai yi takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya ce zai gana da shugaban Koriya ta Arewa domin tattaunawa a kan shirin kasar na kera makamin nukiliya idan ya zama shugaban kasa.

Mista Trump ya ce, "Zan yi magana da shi [Kim Jong-un]; babu wata matsala idan na yi magana da shi.

Hakan dai wani sauyin ra'ayi ne daga Amurka kan kasar ta Koriya ta Arewa.

Sai dai Hillary Clinton, matar da ke son yin takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Democrat, ta soki Mista Trump, tana mai cewa "yana son É—asawa da wasu shugabannin kasashen waje".

Ta kara da cewa shirye-shiryensa kan kasashen waje ba su da muhimmanci.