Shugaban 'yan hamayyar Uganda ya gurfana a kotu

Image caption Masu goyon bayan Besigye sun yi zanga-zanga a gaban kotun.

Shugaban 'yan hamayyar Uganda Kizza Besigye ya gurfana a gaban kotun da ke Kampala, babban birnin kasar, inda ake tuhumarsa da laifin cin amanar kasa.

An karanta masa masa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa, sannan aka dage shari'ar zuwa ranar daya ga watan Yuni.

Mr Besigye ya shaida wa kotun cewa shi zai kare kansa, don haka ba ya bukatar wani lauya ya kare shi.

An girke 'yan sanda da sojoji a titunan da ke kan hanyar kotun, a yayin da ake wucewa da shi zuwa kotun daga gidan yarin da ake tsare da shi.