Amurka za ta gurfanar da Saudiyya a kotu

Majalisar dattawan Amurka ta amince da ƙudirin dokar da zai bai wa iyalan waɗanda harin ranar 11 ga watan Satumba ya shafa a biranen New York da Washington damar shigar da gwamnatin Saudiyya ƙara a gaban kotu.

Yawancin wadanda ake gani suka kai harin na 11 ga watan Satumba 'yan kasar Saudiyya ne, kuma akwai zargi a Amurka na cewa, waɗanda suka kai harin suna da alaƙa da gwamnatin Saudiyya.

Sai dai wani kakakin fadar White House ya ce, Shugaba Obama yana da ja dangane da ƙudirin, kuma da wuya ya sanya masa hannu.

Ƙudirin dai ya yi karo da fushin Saudiyya inda ta yi barzanar janye dimbin dukiyarta daga tattalin arzikin Amurka, idan har aka amince da ƙudirin.