An ƙara gano wata 'yar Chibok

Rundunar sojan Nigeria ta ce, ta ƙara ceto wat daga cikin 'ya matan Chibok fiye da dari biyu da 'yan Boko Haram suka sace.

Kakakin rundunar sojan ƙasar, Kanal Sani Usman Kuka Sheka ya faɗawa BBC cewa, nan gaba kaɗan za bada ƙarin bayani dangane da yarinyar da aka ceto.

Koda ranar yau shugaba Muhammadu Buhari ya gana da yarinyar nan 'yar makarantar Chibok, wadda aka ceto bayan fiye da shekara biyu a hannun 'yan Boko Haram.

An sami yarinyar, mai shekaru 19, tare da jaririyarta 'yar wata huɗu a wani daji da ke kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Yarinyar na daya daga cikin 'yan mata 219 da Boko Haram ta yi garkuwa da su daga makarantar kwana ta Chibok a watan Afrilun shekarar 2014.