Dokar hana shan taba ta fara aiki a Uganda

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Babu tabbas kan yadda 'yan sanda za su tabbatar da aiki da dokar.

Wata doka, wadda ta haramta sayarwa ko shan taba a bainar jama'a a Uganda, ta soma aiki ranar Alhamis.

Za a ci tarar duk wanda aka gani yana shan taba a gidajen giya, ko na abinci, ko kuma otal-otal dalar Amurka sittin ko kuma su yi zaman jarun na abin da zai iya kai wa wata biyu.

Dokar ta tanaji cewa duk mai shan taba dole ya bayar da tazarar akalla mita hamsin tsakaninsa da jama'a.

Dokar ta kuma hana sayar da taba mai lantarki da kuma wacce take da dandano mai kanshi, wadanda ake yayin shan su musamman a Kampala, babban birnin kasar.

Babu tabbas kan yadda 'yan sanda za su tabbatar da aiki da dokar ganin cewa akwai laifuka da dama da suke kokarin magancewa.