An kashe ma'aikatan MDD a Mali

Hakkin mallakar hoto AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe biyar daga cikin ma'aikatan agajin ta, a yayin da uku kuma suka samu rauni bayan wani harin kwanton bauna da aka kai masu a arewacin Mali.

Wata mota da ta fito daga Chadi, dauke da ma'aikatan ce ta yi karo da wani abu da aka dasa mai fashewa, kuma daga bisani wasu 'yan bindiga suka bude musu wuta.

Lamarin ya afku ne a yankin Kidal, matsuguni ga mayakan da ke da tsattsaurar ra'ayin Islama, da kuma 'yan tawayen kasar.

A wata sanarawa da Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar, ta ce jami'anta suna fuskantar hare-hare da dama a wannan yankin cikin shekarar nan.

Shekara uku da suka gabata ma sai da sojojin Faransa suka shiga tsakani domin dakile hare-haren kungiyoyin 'yan ta'adda a Bamako babban birnin kasar ta Mali.