Za a kafa dokar hana zubar da ciki a Amurka

Hakkin mallakar hoto SCIENCE PHOTO LIBRARY

'Yan siyasa a jihar Oklahoma ta Amurka sun kada kuri'ar da za ta sanya dokar haramta zubar da ciki.

Dokar za ta bada damar yankewa duk wani likita da ya jagoranci zubar da ciki hukuncin shekaru 3 a gidan kaso, da kuma hana su sabunta takardar shaidar zama likita.

Majalisar dokokin jihar ta amince da kudurin dokar da rinjayen kashi 33, yayin da wadanda ba su amince ba suke da kashi 22.

Sai dai wakilin BBC a arewacin Amurka yace ko da an amince da dokar, masu fafutuka za su kalubance ta a babbar kotun kasar.

Jihar Oklahoma ce ta baya-bayan nan a Amurka da aka tsaurara matakan zubar da ciki.