Boko Haram ta kashe mutum 20 a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Boko Haram sun kona kasuwa da masallacin garin.

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kashe akalla mutum 20 a wani hari da suka kai a garin Yebi na yankin Bosso ranar Alhamis da daddare.

Ganau sun ce mayakan kungiyar ta Boko Haram sun kuma kona kasuwa da unguwar da ke kusa da ita da kuma masallacin Juma'a na garin.

Sun kara da cewa mutane da dama sun jikkata sanadin harin.

Yankin na Bosso dai ya sha fama da hare-haren kungiyar ta Boko Haram.

Jamhuriyar Nijar na cikin kasashen da suka hada gwiwa domin yakar kungiyar ta Boko Haram.