Ma'aikatar shari'a na yajin aiki a Ghana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar Ghana, John Mahma, lokacin da yake shan rantsuwar shiga ofis.

Kotuna a duk fadin Ghana sun kasance a rufe sakamakon wani yajin aikin da ma'aikatar sha'riar kasar ta fara daga ranar Juma'a.

Jami'an ma'aikatar shara'ar dai na son matsawa gwamnati lamba ne domin ta biya su dukkanin wasu hakkokinsu.

Ma'aikatan dai suna neman gwamnati da ta biya su alawus-alawus dinsu a kan lokaci.

A cikin watan Afrilun da ya wuce ne dai ma'aikatan suka janye wani yajin aiki da suka fara bayan da gwamnati ta yi alkawarin biyansu dukanin albashinsu to amma sai hakan bai yi wu ba.