Tsawon kwana na ruɓanya a Afirka — WHO

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan Nigeria kan iya rayuwa shekara 54 da 'yan watanni

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce tsawon ran 'yan Afirka yana ruɓanyawa fiye da na sauran sassan duniya.

Wani rahoton da hukumar ta fitar ya ce tun daga shekarar 2000 ake samun hauhawar tsawon ran, a nahiyar ta Afirka.

Yanzu haka, matsaikatan shekaru da 'yan Afirka ke yi a duniya su ne 60. Amma al'amarin ba haka yake ba, a ƙasashen da suke da wadata, a inda shekara 40 ne matsakaitan shekarun da mutane ke yi.

Wani jami'in hukumar ta WHO, Dr Ties Boerma ya alakanta dalilin tsawon ran da irin yadda allurar rigakafi ta rage mutuwar ƙananan yara a Afirka.

Image caption Al'ummar Algeria ne ke da shekarun da suka fi na kowa a Afirka, a ida suke rayuwa har shekara 75 da 'yan watanni

Al'ummar ƙasar Algeria ne dai suke kan gaba wajen daɗewa a duniya, a inda 'yan ƙasar sukan iya rayuwa har fiye da shekara 75.

Ethiopia ce ta 16, a inda 'yan kasar kan mutu a shekara 64 da wata 8. Kenya ce ta 22 kuma al'ummarta na mutuwa a shekara 63 da wata 4.

Mutanen Ghana ka iya zama a duniya har shekara 62 da wata 4 kuma hakan na nufin ita ce ta 25 a jerin kasashen.

Hakkin mallakar hoto AFP GETTY
Image caption Somalia ce kurar baya, a inda mutanenta kan mutu daga 47

Somalia ce ta 47 da shekara 55, a inda Nigeria ta zamo ta 48 saboda 'yan kasar na mutuwa daga shekara 54 da wata 5. Sierra Leone ce kurar baya, a inda al'ummarta ke mutuwa daga shekara 50 da wata ɗaya.

Ƙasashe 10 da mutanensu suka fi daɗewa a duniya:

  • Algeria - 75.6
  • Tunisia - 75.3
  • Mauritius - 74.6
  • Morocco - 74.3
  • Cape Verde - 73.3
  • Seychelles - 73.2
  • Libya - 72.7
  • Egypt - 70.9
  • Sao Tome - 67.5
  • Senegal - 66.7