Tsohon shugaban NIMASA zai sha daurin shekaru 5

Hakkin mallakar hoto NIMASA

A ranar Juma'a ne babbar kotun tarayya a jihar Legas ta yanke hukuncin shekaru biyar ga tsohon shugaban hukumar kula da sufurin jiragen ruwa, Mista Raymond Temisan Omatseye, bisa samunsa da laifin almundahanar kudi,fiye da Naira biliyan 5.

An gurfanar da Mr Omatseye a gaban kuliya ne kan tuhumar aikata laifuka 27 da suka jibanci zargin jirkita bayanan kwantiragi da na zabe da kuma bayar da kwangilar da ta wuce ikonsa.

Lokacin da koma ga saurarar karar a ranar 14 ga watan Maris , mai shigar da kara, Godwin Obla da kuma lauyan Mr Omatseyen, E.D Onyeke sun gabatar da bahasinsu na karshe, sannan kuma suka mika shi ga kotun a rubuce.

A baya dai lauyan Mr Omatseye dai ya bukaci kotun ta yi watsi da karar, bisa dalilin cewa masu shigar da karar ba su kawo wasu sahihan hujjoji game da zarge-zargen da ake yi masa ba.

To amma mai gabatar da kara Mr Godwin Obla ya hakkake cewa duk laifukan na da kwararan hujjoji, kuma suna da tabbacin cewa Mr Omatseye ya aikata duk laifukan da ake zarginsa da shi.