G7:Dole mu dakile hanyoyin kudi na yan ta'adda

Hakkin mallakar hoto

Ministocin kudi na kasashe bakwai masu cigaban masana'antu na duniya (G7) sun amince da sabbin matakai domin dakile hanyoyin da yan ta'adda na kasa da kasa ke samun kudade.

Haka kuma Ministocin sun gabatar da wani shiri da ya bukaci karin musayar bayanan sirri da tsaurara dokoki kan kudaden da aka yi musayar su a tsakanin kasa da kasa da kuma karin hadin kai wajen rike kadarorin da yan ta'adda suka mallaka.

Ministocin wadanda ke taro a Japan sun kuma bukaci kasashe su kaucewa gogayyar rage darajar kudadensu sun kuma yi gargadin cewa ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar turai zai jefa tattalin arzikin duniya cikin wani wadi.

Taron na kwanaki biyu da ke gudana a arewacin birnin Sendai na zuwa ne gabanin taron kolin shugabannin kasashen na G7 wanda zaa yi a Japan.