Taro kan wa'azi lokacin Azumi a Kaduna

Gwamna Nasiru El-Rufa'i Hakkin mallakar hoto kaduna govt
Image caption Taron na zuwa ne makwanni kadan kafin watan Azumi.

Majalisar limamai da malaman jahar Kaduna na gudanar da taro ne gabanin fara Azumin watan Ramadan.

Malaman na magana ne a bisa yadda ya kamata a gudanar da Tafsiri a cikin hikima, haka kuma Malaman na cewa ya kamata yan Kasuwa su rangwantawa jama'a dan samun sassaucvin kayan masarufi a lokacin Azumi.

Sun kuma duba batutuwa na kasar kamar yaki da cin hanci da rashawa, da batun yan kungiyoyin ta'adda na yankin Naija Delta wadanda malaman suka ce ya kamata a fuskance su kamar yadda aka fuskanci Boko Haram.

Batun halin matsin tattalin arzikin da suka ce jama'a na ciki ya janyo talauci tsakanin al'uma.

Sun kuma bukaci shugaba Buhari da ya duba batun cire tallafin Mai da gwamnati ta yi sosai, da kuma yin tankade da rairaya cikin masu bashi shawara, saboda akwai masu yi masa zagon kasa.