Amurka na jin an kashe shugaban Taliban

Image caption Jagoran Taliban Mullah Mansour

Manyan hafsoshin sojin Amurka sun ce dakarunsu sun kai hari ta sama a kan jagoran Taliban a Afghanistan, Mullah Akhtar Mansour.

Sun ce suna kyautata zaton cewa Mullah Akhtar Mansour ya rasu.

An dai yi amfani da jirage marasa matuka masu yawa wajen kai musu hari shi da wani mutum a cikin mota lokacin da suke kokarin ratsa wani sunkuru, kusa da Ahmad Wal da ke kan iyakar Afghanistan, suna neman shiga kasar Pakistan.

Kakakin Pentagon ya ce Mullah Akhtar Mansour barazana ne ga rundunar sojoji da fara-hula, kana yana yin cikas ga kokarin wanzar da zaman lafiya.

A watan jiya ne mayakan Taliban suka fara kai sabbin hare-hare a Kabul da wasu birane.