MDD:Ana kai wa makarantunmu hari

Hakkin mallakar hoto Reuters

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan rabin makarantun da take gudanarwa a Gabas Ta Tsakiya ga Falasdinawa 'yan gudun hijira an kai musu hari, an lalata su ko kuma an tilasta musu rufe makarantun a cikin shekaru biyar da suka wuce.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Falasdinawa yan gudun hijira ta ce lahani mafi muni da aka yiwa makarantun shine a Syria inda aka rufe fiye da rabin makarantun da ta ke gudanarwa.

Hukumar ta ce wasu makarantun sun lalace wasu yaki ya sa ba a komai a cikinsu wasu kuma an tsugunar da mutanen da suka rasa muhallansu.

Ta ce a halin da ake ciki an sami tsaiko ga ilmin dubban yara