Ana takaddama kan cutar Zika a Amurka

Hakkin mallakar hoto Roger Eritja

Hukumomin kiwon lafiya na Amurka, sun furta cewa, an dai gudanar da gwaji ga mata masu juna biyu su dubu dari biyu da 79.

Dukan matan sun nuna alamar cewa sun harbu da kwayar cutar.

Wannan abun dai zai kawo wani babban cikas a bagaren haihuwa.

Shugaba Obama, ya na nuna damuwa ganin yadda majalisar dattawan Amurka ta amince da rabin kudin da ya nema.

To sai dai kuma majalisar wakilai daga nata bangare ta amince ne kawai da kashi daya cikin uku na abun da shugaban ya tambaya.

Shugaban ya kara da cewa, ko wadannan kudin ma an karkato su ne daga assusun gwagwormaya da barazanar Ebola.

Obama ya yi korafi mai kaifi ga yan majalisar Amurka game da yin abun da ya danganta da yin kasa a gwiwa da su ka yi kan amincewa su da bukatar ta shi.