An kashe Shugaban Taliban Mansour

Mullah Mansour
Image caption Shugaban Taliban Mullah Mansour

Jami'an leken asiri a kasar Afghanistan sun tabbatar cewa an kashe jagoran Taliban Mullah Akhtar Mansour,a harin da jirgin sama mara matuki na Amurka ya kai.

Tun farko, Amurka ta ce tana jin ta kashe Mansour a harin da ta kai a Pakistan, kusa da kan iyakar Afghanistan.

Sakataren harkokin waje na Amurka, John Kerry, ya ce Mullah Mansour wanda shi ne jagoran Taliban tun daga watan Juli na shekarar 2015 na cigaba da yin barazana ga jami'an Amurka da ke Afghanistan da kuma jami'an tsaron kasar da fararen hula.

An sanar da Afghanistan da Pakistan a hukumance ne bayan da aka kai harin.