Girka ta amince da sauye-sauye a kan tattalin arziki

Malisar dokokin Girka ta amince da wasu sauye-sauye da suka shafi tattalin arzikin kasar bayan watan zazzafar muhawara da aka shafe kwana hudu ana tabkawa a kan daukan matakan tsuke aljihun gwamnati.

Firai Ministan kasar Alexis Tsipras ya bayyana matakin da majalisar ta dauka da cewar alama ce ta irin dukufar kasar wajen cika alkawuran da ta yi da suka shafi tattalin arziki.

Ya ce yana da kwarin-gwiwar cewa yanzu kasashe masu amfani da Euro za su amince a kara wa kasarsa kudin da take bukata domin ta biya bashin da ta ci daga hukumar ba da lamuni ta duniya.

Dubban jama'a dai sun yi zanga-zangar adawa da wannan mataki a wajen harabar majalisar dokokin kasar.