Sojojin Iraqi sun kudiri kwato garin Falluja

Sojojin Iraqi sun umarci mazauna birnin Falluja wanda ke karkashin ikon kungiyar IS da su fara shirin ficewa daga birnin.

Rundunar sojin ta bada shawarar ce gabanin gagarumin farmaki da za su kaddamar domin sake kwato birnin.

Wani shafin Internet Shafaq mai goyon bayan Kurdawa yace tuni sojoji kimanin 20,000 suka isa kewayen Falluja.

Kungiyar kare hakkin bil Adama Human Rights Watch wadda ke da mazauninta a Amurka ta ce mutanen da suka makale a Falluja suna fama da matsanancin karancin abinci.

Ga rahoton da Halima Umar Saleh ta hada mana:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti