Iraki: An umarci mutanen Falluja su bar birnin

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun tsaro 25,000 za su fafata da mayakan IS a Falluja

Rundunar sojin Iraki ta umarci mazauna birnin Falluja wanda ke karkashin ikon mayakan kungiyar IS da su shirya barin garin.

Sojojin sun bayar da wannan shawara ce gabannin wani hari da suke tsammanin kai wa domin kwato birnin daga hannun IS.

Wani shafin intanet na Kurdawa Shafaq, ya ce kusan dakarun tsaro 25,000 ne suka isa wajen birnin na Fallujah.

Ga rahoton da Halima Umar Saleh ta hada mana:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Karin bayani