NLC ta dakatar da yajin aiki a Nigeria

Image caption An dai samu rarrabuwar kawuna tsakanin kungiyoyin kwadago kan yajin aiki a Nigeria

Kungiyar kwadago ta kasa a Najeriya NLC, ta dakatar da yajin aikin gama gari da ta shiga.

Mataimakin kakakin kungiyar NLC, Nuhu Abbayo Toro shi ne ya tabbatar wa da BBC hakan.

NLC dai ta shiga yajin aikin ne a ranar Larabar da ta gabata, domin nuna rashin amincewa da karin kudin man fetur da na latarki da gwamnati ta yi a kasar.

Kungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aiki ne bayan wani taron gaggawa da ta kira ranar Lahadi a Abuja.

Ana fatan kungiyar za ta koma kan teburin tattaunawa da gwamnati domin daidaitawa.