PDP ta naɗa Maƙarfi sabon shugaba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption PDP ta nada Makarfi ne bayan sauke Modu Shariff

Jam'iyyar adawa ta PDP a Nigeria, ta nada tsohon gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Makarfi, a matsayin shugabanta na wucin gadi.

Jam'iyyar ta yi wannan nadin ne a babban taronta da ta gudanar ranar Asabar a Fatakwal da ke jihar Rivers, inda ya maye gurbin Sanata Ali Modu Sheriff.

Sai dai wani bangare na jam'iyyar da shi ma ya gudanar da nasa taron a birnin Abuja, ya nada Sanata Ibrahim Mantu, a matsayin shugaban jam'iyyar ta PDP.

Barista Bashir Maidugu shi ne mataimakin mai bai wa jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a, kuma ya yi wa Raliya Zubairu karin bayani:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti