An nemi Jonathan da Ngozi su yi bayani kan N30tr

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An ambato sunan Ngozi a cikin badakalar $2.1bn da ake zargin Sambo Dasuki da wawurewa.

A Najeriya, masana sun yaba kan matakin da wata babbar kotun kasar da ke Legas ta dauka na umartar tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan da tsohuwar ministar kudi Ngozi Okonjo-Iweala su yi bayani kan yadda aka kashe Naira Tiriliyan 30.

Babbar kotun ta bayar da umarnin ne bayan kungiyar SERAP mai yaki da cin hanci ta nemi kotun ta tilastawa mutanen biyu su yi wa 'yan Najeriya jawabi kan yadda aka kashe kudaden.

Ta bukaci mutanen su yi bayani nan da kwana bakwai.

Kotun ta kara da cewa SERAP tana da hurumin tambayar tsofaffin jami'an na gwamnati su sanar da 'yan kasar yadda aka kashe kudaden.

Kungiyar ta ce an kashe kudaden ne a cikin shekaru hudu kadai, tana mai cewa akwai alamar tambaya kan yadda aka kashe su