Turkiyya:Jam'iyyar AKP ta zabi sabon shugaba

Hakkin mallakar hoto AP

An zabi wani na hannun daman shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a matsayin shugaban jam'iyyar AKP mai mulki.

Zaben Binali Yildirim ya share fagen nada shi mukamin Firaminista.

Mr Yildirim yace babban kudiri ga Turkiyya shine sauya kundin tsarin mulki domin baiwa shugaban kasar karin karfin iko.

Wanda ya gabaci Mr Yildirim wato Ahmet Davutoglu ya yi murabus daga mukaminsa bayan da ya ki amincewa da burin Mr Erdogan na kara wa kansa karfin iko matakin da masu sukar lamirin gwamnatin suka ce zai yi karan tsaye ga dimokradiyya.

Mr Yildirim yana kuma goyon bayan cigaba da kai farmakin soji a kan mayakan Kurdawa.