Mutum 37 sun mutu a Zambia

Image caption Shugaban Zambia Edgar Lunga

Mahukunta a Zambia sun ce a kalla mutum 37 ne suka mutu a wani hatsarin da wata motar safa ta yi a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo.

Kazalika, sama da mutum 20 sun jikkata a hatsarin.

Rahotannin sun ce motar na kazamin gudu ne lokacin da ta ci karo da wani shuri da ke kusa da iyakar kasar da Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo, kuma nan take ta kama da wuta.

Motar safar dai mallakin mutanen Zambia ce.