Asirin Minista ya tonu a Brazil

Hakkin mallakar hoto Ag Brasil

Wani babban Minista a Brazil ya yi murabus, bayan an nadi maganarsa a faifai, ana zargin yana kitsa makircin yadda za a hana-ruwa-gudu a binciken badakalar cin hanci mafi girma a kasar.

Cin bayanin da aka nada, wanda wata jaridar kasar ta fitar, Ministan mai suna Romero Juca ya ce tsige shugabar kasar da aka dakatar daga mukaminta, wato Dilma Russeff zai taimaka wajen dakatar da bincinken cin hancin da ake yi a kan kamfanin man kasar na Petrobras.

Sai dai Romero Juca ya ce an juya masa maganar da ya yi, kuma yana goyon bayan binciken da ake yi.

Ministan dai na hannun daman shugaban rikon-kwaryar kasar ne, wato Michel Temer.

Ita ma Mrs Dilma Russeff, a nata bangaren ta ce yunkurin tsige ta daga mukaminta wani juyin-mulki ne irin na siyasa da aka shirya domin a kare wasu manya a kasar, wadanda ke da hannu a badakalar kamfanin Petrobras.