China na jinyar makanta da fatar idon Alade

Sinawa masana kimiyya sun samar da wata hanyar jinyar masu makanta ta amfani da kwayar idon Aladu sakamakon karancin abubuwan da ake amfani da su wajen dashen-ido ga bil'adama.

Kimanin mutum miliyon biyar ne ke fama da matsalar lalacewar fatar da ke rufe kwayar ido a China, ga shi ana fama da karancin mutanen da za su ba da gudummuwar tasu domin yi wa masu bukatar dashen ido mutum 5000 a kowace shekara.

An fara amfani da sabuwar hanyar dashen kwayar idon ne a fadin kasar, bayan amincewar da gwamnati ta yi da yin hakan tun a bara.

Ana dai tsabtace fatar kwayar idon aladun ta hanyar kashe duk kwayoyin cututtukan da ke jiki gabannin yin dashen..

Sai dai masu sukar wannan hanyar jinyar na cewa kasar China na ci-da-zuci ba tare da la'akari da hadarin da ka iya biyo baya ba.