Ana karancin mai a Faransa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun makon da ya gabata ake zanga-zanga a Faransa

Ana cigaba da karancin man fetur a Faransa, kwanaki biyar bayan masu zanga-zanga sun rufe matatun mai da defo-defo na kasar domin neman sauya dokokin daukar aiki.

Ma'aikatar sufuri ta kasar ta ce, akwai isasshen man fetur din da zai isa ya magance wahalarsa da ake ciki.

Gwamnati ta ce sauye-sauyenta za su rage yawan marasa aikin yi.

Amma matakin bai samu karbuwa ba a wajen kungiyoyin kwadago da magoya bayan jam'iyyar Socialist gurguzu.

Karin bayani