An kama 'yar kunar bakin wake a Kano

Hakkin mallakar hoto
Image caption An sha kai hare-haren kunar bakin wake sassa daban-daban na Najeriya

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce tana cigaba da kula da wata mata da aka ce an sato daga Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya, da nufin kai harin kunar bakin wake.

Matar dai ta ce kubuce ne daga mutanen da suka sato ta yayin da ta farfado daga baccin da suka sanya ta, sannan suka shaida mata cewa za ta yi musu aikin Allah a kasuwa.

A yanzu haka dai rahotanni na cewa an tsaurara tsaro a birnin na Kano da ma jihar baki daya.

Ahmad Abba Abdullahi ya tuntubi wakilinmu na Kano Yusuf Ibrahim Yakasai, inda ya yi karin bayani dangane da wannan lamari:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti