Mutane 3 sun mutu a zanga-zangar Kenya

Hakkin mallakar hoto

Rahotanni daga Kenya sun ce an kashe mutane uku a lokacin wata zanga zangar da aka yi kan hukumar zaben Kasar.

Masu goyan bayan 'yan adawa sun bazama kan tituna a karo na hudu, suna bukatar kwamshinan hukumar zaben Kasar ya yi murabus saboda zarge zargen cin hanci da rashawa da kuma nuna son kai.

Wani mutum ya mutu a birnin Kisumu na yammacin kasar.

Majiyoyin 'yan adawa sun ce 'Yan Sanda ne suka kashe shi, amma jami'ai sun ce tuntube ya yi ya fadi a lokacin da yake gujewa 'yan adawar.

An bada rahotan kashe karin mutane biyu a kusa da Siaya.

A yankin Kibera dake Nairobi babban birnin kasar, 'Yan Sanda sun fesa hayaki mai sa hawaye domin hana masu zanga- zangar shiga cikin ofisoshin hukumar.

Jam'iyyar adawa ta CORD ta zargi hukumar da nuna son kai, amma kwamishinonin hukumar sun hakikance cewa za su sa ido a kan zaben Shugaban Kasar da za a yi shekara mai zuwa