An gano sabuwar almundahana a NNPC

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Kamfanin NNPC bai mayar da martani ba tukunna a kan batun

Hukumar da ke sa ido don tabbatar da gaskiya a bangaren ma'adinai ta Nigeria, NEITI, ta zargi kamfanin mai na NNPC da kin saka dala biliyan 3.8 da kuma Naira biliyan 358.3 a aljihun gwamnatin tarayya a shekarar 2013.

NEITI ta ce ta gano hakan ne a wani binciken kudi na baya-bayan nan da ta gudanar.

A ranar Lintinin ne dai Shugaban hukumar ta NEITI, Kayode Fayemi, ya bayar da sanarwar a Abuja a lokacin da yake gabatar da binciken kudin hukumar na shekarar 2013.

A yayin da yake bayani, Mista Fayemi ya ce hukumar ba ta samu wadansu kudaden shiga da ya kamata a ce sun shiga aljihun gwamnatin tarayya ba--watakila sun bata sakamakon wasu dalilai.

Ya ce, "An samu wadannan basussuka ne da suka taru sakamakon rashin biyan kudaden sayar da rijiyoyin mai da sauran kudaden daga wadansu kamfanonin da ke karkashin NNPC din.''

Wannan dai ba shine karo na farko da aka tuhumi kamfanin NNPC da irin wannan batu na almundahanar kudi ba.