Ranar yoyon fitsari ta duniya

Image caption Mata da dama na fama da yoyon fitsari a Nijar

Ranar Litinin ne Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin fadakar da al'umma a kan illolin cutar yoyon fitsari.

Masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa aurar da yara mata a kananan shekaru na daga cikin dalilan da ke haddasa wannan cuta ta yoyon fitsari.

Jamhuriyyar Nijar na daga cikin kasashen Afrika inda wannan matsalar ta yi kamari, duk da cewa hukumomi na cewa an fara samun raguwar wannan matsala.

Wakilinmu Baro Arzika a Yamai, ya ziyarci cibiyar kula da mata masu yoyon fitsari da kungiyar Dimol ta kafa a Yamai, ga kuma karin bayanin da ya aiko mana:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti