Rikicin PDP bai zo wa masana da mamaki ba

Masana al'amuran siyasa a Najeriya sun ce rikita-rikitar da ta gigita jam'iyyar adawar kasar, wato PDP, ba ta ba su mamaki ba.

Rikicin shugabancin da jam'iyyar ta fada ciki a baya-bayan nan dai ya yi kamari bayan mutum uku, kowannensu na ikirarin cewa shi ne shugaban jam'iyyar.

Tuni dai rundunar 'yan sandan Najeriya ta gargadi shugabannin jam'iyyar da mabiyansu da su guji ta da zaune tsaye.

Dr Abubakar Kari malami ne a tsangayar kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja, ya kuma bayyana wa Muhammad Kabir Muhammad yadda yake kallon wannan takaddama ga kuma hirar ta su.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti