'Yan sanda sun gargaɗi PDP

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sanda sun ce za su sanya kafar wando daya da 'yan PDP.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gargadi 'yan PDP, babbar jam'iyyar hamayya ta kasar da su guji tayar da hankali ko kuma ta sanya kafar wando daya da su.

Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan, Olobisi Kolawole ta aikewa kafafen watsa labarai, ta ce rundunar ta samu bayanan sirri da ke nuna cewa shugabanni da mambobin bangarorin jam'iyyar ta PDP suna wani shiri na tayar da hankalin 'yan kasar ta hanyar amfani da 'yan daba a Abuja ranar Litinin.

Rundunar ta kara da cewa 'yan PDPn suna yin wani shiri na shiga Abuja, sannan su mamaye hedikwatar jam'iyyar saboda sabanin da ke tsakanin bangarorinsu.

A cewar rundunar 'yan sandan hakan ne ma ya sa Babban Sifetonta ya bayar da umarni a girke dakarunsu a hedikwatar domin dakile duk wani yunkuri na yin hakan.

A karshen makon da ya gabata ne dai jam'iyyar ta PDP ta fada sabon rikici sakamakon cire shugaban rikonta, Sanata Ali Modu Sheriff da kuma maye gurbisa da Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, tsohon gwamnan jihar Kaduna da aka yi.

Gabanin hakan dai, PDP ta fada rikicin shugabanci bayan Ali Sheriff ya ce ba zai sauka daga shugabancin jam'iyyar ba, duk kuwa da cewa wa'adin da aka dibar masa ya kare, lamarin da ya sa wasu 'yan mja'iyyar suka gurfanar da shi a gaban kotu.