Za a daukaka kara kan shari'ar Jacob Zuma

Hakkin mallakar hoto

Masu shigar da kara a Afirka ta Kudu sun ce za su daukaka kara kan hukuncin da kotu ta yi na cewa ya kamata a tuhumi shugaba Jacob Zuma kan cin hanci da rashawa.

Da farko dai, an janye tuhumar da ake masa makonni kafin zaben da aka yi a shekarar 2009 wanda ya yi sanadiyar ya zama shugaban kasar.

Sai dai a watan da ya gabata wata babbar kotu ta bayyana cewa hukuncin da aka yanke a wancan karo bai dace ba.

Wani alkalin kotun, Judge Aubrey Ledwaba, ya bukaci Hukumar shigar da kara ta kasar, NPA, ta duba yiwuwar sake bude shari'ar.

Mista Zuma ya sha musanta zargin da ke yi masa na karbar hanci a badakalar sayen makamai da darajarsu ta kai biliyoyin daloli a shekarar 1999.