An kashe mutum sama da 100 a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP

An tayar da wasu jerin bama bamai a cikin mota sannan kuma an kai hare-haren kunar bakin-wake a birane biyu da ke gabar teku a yankin Latakia da ke hannun gwamnatin Syria.

Masu fafutuka sun bayyana cewa mutum fiye da 100 sun mutu bayan fashewar wasu abubuwa kusa da tasoshin motocin safa a Tartous da kuma Jableh -- wadanda a baya ba sa cikin jerin wuraren da ake rikici.

An kuma bayar da rahoton cewa an kai wani hari a wani asibiti a Jableh.

Wata kafar yada labarai ta kungiyar mayakan IS ta yi ikirarin kai hare-haren.

Rasha, wacce take marawa Shugaba Asad baya, na da sansanin sojin ruwa a Tartous, yayin da sansaninta na sama ke kusa da Jableh.

Wani kakakin gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov, ya ce hare-haren na nuni da bukatar ci gaba da tattaunawar zaman lafiya a Syria.