Fafaroma ya gana da limamin Azhar

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ganawar babban limamin Al-Azhar da Fafaroma Francis

Fafaroma Francis ya yi wata tattaunawa da manyan shugabannin mazhabar Sunna ta Musulunci a fadar Vatican, domin kyautata alaka tsakanin manyan addinan duniya biyu, wato Musulunci da Kiristanci.

A farkon ganawar da ya yi ta minti 30 da babban limamin masallacin Al-Azhar na Alkahira a kasar Masar, Sheikh Ahmed el-Tayyib, Fafaroman ya ce tattaunawar na da matukar muhimmanci.

Wannan tattaunawa na zuwa ne bayan shekara biyar da hukumar Al-Azhar ta yanke duk wata alakar ganawa da fadar Vatican domin nuna fushinta kan abin da ta kira kalaman adawa da Musulunci da tsohon Fafaroma Benedict ya yi.

Addinan Musulunci da na Kirista su ne manyan addinan duniya da ake yawan samun sabani tsakanin mabiyansu a bangarori daban-daban.

Karin bayani