Australia na yaki da Jemagu

Mahukunta a jihar New South Wales ta kasar Australia sun ayyana dokar ta-baci domin ta taimaka wajen yaki da wasu dubban Jemagu da suka mamayi wani gari mai suna Bateman's Bay.

Mazauna garin sun ce Jemagun sun addabe su da yawan kuka, da wari da kuma kazamar tuka.

Mahukuntan jihar dai na shirin kashe dala miliyon daya da dubu dari takwas wajen tarwatsa Jemagun.

Dandazon jemagu dai kan yi kwamba a garin Bateman's Bay a duk lokacin da itatuwa ke yin fure.