Kai-tsaye: Bikin cikar Buhari shekara ɗaya

Ku latsa nan domin sabunta shafin

1029: Jam'iyyar PDP da ke hamayya a Najeriya ta ce babu abin da Shugaba Buhari ya yi illa bata kasar a shekara guda da ya yi a kan mulki.

0857: Ku saurari ra'ayoyin wasu 'yan kabilar Igbo kan shekara guda ta gwamnatin Buhari:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Daya daga cikin batutuwan da aka fi tattaunawa a kansu a shafukan Twitter na Najeriya shi ne #PMBWasted365Days, wato Kwana 365 Da Buhari Ya Bata.

0805: Ra'ayin Muhammad Hussaini Imu shi ne, " Ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya sani cewa muna cikin mawuyacin hali."

0749: Bello Umar Shira ya aiko mana sako ta Facebook, inda ya ce "Shugaba Buhari ya kamata ka bibiyi yarjejeniyar da Marigayi Umaru Musa 'Yar'adua ya yi da tsagerun Naija Delta domin yi musu na afuwa. Wannan shi ne kadai abin da zai kawo karshen fitinar nan".

0745: Mai binmu a shafin Facebook, Mubarak Sani Kankia, ya aiko da sako ta shafin inda yake cewa "Ina yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari addu'ar Allah ya ba shi ikon cika alkawuran da ya daukarwa al'umman Nigeria."

0734: Shugaban Najeriya ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka ceto biyu daga cikin 'yan matan Chibok 219 da Boko Haram ta sace a shekarar 2014.

0730: Muhammadu Buhari ya kammala jawabin da ya yi wa 'yan Najeriya, amma za mu ci gaba da kawo muku abubuwan da ya fada daki-daki.

0728: Shugaba Buhari ya jaddada aniyarsa ta farfado da tattalin arzikin Najeriya.

0716: Buhari ya ce zai sa a kama masu tayar da kayar-baya a yankin Naija Delta wadanda suke fasa bututan man Najeriya.

Image caption Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta gaji dimbin matsaloli daga gwamnatin da ta gabata, yana mai cewa yana yin bakin kokarinsa wajen ganin ya komo da Najeriya kan turba.

0710

0700: Shugaba Buhari ya soma jawabi ga 'yan Najeriya kan cikar gwamnatinsa shekara daya a kan mulki.

0650: Da misalin karfe bakwai na safiyar nan Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi kai-tsaye ga 'yan Najeriya kan cikar gwamnatinsa shekara daya a mulki.

Hakkin mallakar hoto NTA

A ranar Lahadi ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke cika shekara daya da fara mulki. Shin kwalliya ta fara biyan kudin sabulu?