CBN ya fitar da sabon tsari kan musayar kudi

Hakkin mallakar hoto cbn facebook page

Babban bankin Nigeria, CBN, ya bullo da wani sabon tsari a fannin kasuwar hada-hadar musayar kudaden kasashen waje ta kasar.

Shugaban babban bankin Najeriyar, Godwin Emefiele ya ce an yi hakan ne domin inganta harkar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.

Ya kara da cewa hakan kuma wani yunkuri ne na dakile koma bayan tattalin arzikin kasar.

Mista Emefiele ya ce kwamitin kula da tsare-tsaren manufofin kudade na kasar, ya amince a sauya al'adar da kasar ta saba da ita ta sauya dala daya a kan Naira 197.

Sai dai bai yi cikakken bayani a kan yadda bankin zai gudanar da wannan sabon tsari ba.

Tun bayan da farashin danyen mai ya fadi a kasuwannin duniya, kana darajar naira ta fadi, wasu masana suka yi ta kira ga babban bankin ya rage darajar kudin kasar.