Kotu ta sauke Makarfi daga shugabancin PDP

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rikici ya ki ci ya ki cinyewa a PDP

Wata babbar kotu a jihar Lagos da ke kudu maso yammacin Nigeria, ta sauke Sanata Ahmad Makarfi daga shugabancin riko na jam'iyyar PDP.

Alkalin kotun, Ibrahim Buba, ya kuma bayar da umarnin mayar da Sanata Sheriff kan shugaba.

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka nada Sanata Makarfi a matsayin shugaban riko na jam'iyyar bayan an sanar da sauke Sanata Ali Modu Sheriff.

A makon ne da ya gabata ne aka yi ta samun sabani a jam'iyyar ta PDP, inda wani bangaren ya dora Sanata Makarfi a matsayin shugabanta, kwamitin dattawa kuma ya ce Sanata Nasiru Mantu ne nasa shugaban, yayin da Sanata Ali Modu Sheriff kuma ya ce shi ma yana nan daram.

Lamarin dai ya sa sai da rundunar 'yan sandan kasar ta jibge jami'anta a hedikwatar jam'iyyar ta PDP da ke Abuja domin hana barkewar rikici.