Bunkasa ilimi a yankunan da ake yaki

An kaddamar da taimakon kudi na gaggawa domin samar da ilimi a yankunan da ke fama da rikice-rikice da balao'i a wajen babban taro na duniya kan ayyukan jin kai.

Tsohon Firai ministan Biritaniya, Gordon Brown, wanda a yanzu shi ne jakadan Majalisar Dinkin Duniya na mussaman kan ilimi na duniya ne yake jagorantar shirin.

Manufar ita ce a tara dala biliyan 3.8 a cikin shekara biyar masu zuwa, wanda zai tallafawa ilimin mutane sama da miliyan 13.

Mista Brown ya ce hakan zai sa iyalai 'yan gudun hijira su samu kwarin gwiwa.

A lokacin da yake magana a wurin taron a birnin Santanbul na Turkiyya, Mista Brown ya ce: "A karon farko, mun bude asusun neman kudi kan ayyukan agaji da ake sa ran yin amfani da su ta fannin ilimi.

"Kudin da ake nema ba wai na amfanin tsawon mako ko wata guda bane, a'a na tsawon shekaru ne domin tallafawa cigaban yara,'' in ji Mista Brown.

Kuma za a ajiye wani bangare na kudin ko da a gaba wani bali'in zai faru, ba sai ana yawo da kokon bara ba."

Mista Brown ya kara da cewa ilimi wata hanya ce ta hana yin amfani da kananan yara wajen yin wasu abubuwan da basu da ce ba.

"Ya ce idan ba makaranta, kananan yara da rikici ke ritsawa da su suna fuskantar hadarin zama leburori, ko a yi musu auren wuri ko su zama mayakan sa kai ko ma'aikatan 'yan ta'adda da kuma samun tsaurin ra'ayi.''

Tallafin da ake nema mai taken, "Ilimi ba zai iya jira ba,'' munafarsa shine samar da ilimi ga yaran da rikici ya ritsa da su a kan kari.

Shirin wanda aka kaddamar da neman tallafin dala miliyan 100, ya samu goyon bayan hukumar kula da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban hukumar Irina Bokova, ya ce ana bukatar matakai na musamman cikin gaggawa domin cimma bukatun ilimi na miliyoyin yara da matasa wadanda rikice-rikice da bala'o'i da rashin muhalli ya sa basu da makama a rayuwarsu.

Gabanin taron ne, hukumar kula da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, Unesco, tare da hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya suka wallafa wasu alkaluma da ke nuna cewa kashi 50 cikin 100 na yara 'yan gudun hijira suna makarantar firamare yayin da kashi 25 cikin 100 na yaran wadanda suka mallaki hankalinsu suna makaratar sakandare.

Wani rahoton ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun wasu munanan matsalolin wanda ba a da masaniya sosai a kansu.

Hukumomi masu aiki a sansanin 'yan gudun hijira ne suke tara bayanai a kan ilimin 'yan gudun hijira, amma kuma 'yan gudun hijira da dama basa zama cikin wadannan sansanin 'yan gudun hijirar, suna zama ne a birane ko wasu matsugunai da gwamnati ba ta lamunce da su ba.

Ba a kuma san adadin matasa wadanda suka rasa muhallansu a cikin kasashensu ba kamar yara mata 'yan makaranta wadanda suka bata sanadiyar harin da kungiyar Boko Haram ta kai makarantarsu.

A wani rahoto da Hukumar da ke kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa gabanin taron, ya yi magana kan barazanar da hare-hare ke yi a kan makarantu.

Ya yi gargadin cewa a kullum a kan kai hari kan makarantu ko asibitoci da sojoji ke zama a ciki.

Afshan Khan wani babban jami'i ne a hukumar Unicef, ya ce, "Hari a kan makarantu ko asibitoci a lokacin rikici abin kunya ne kuma abin tayar da hankali ne da ke cigaba da faruwa".

Mista Khan ya kara da cewa hare-haren da kasashen duniya ke kai wa da wadanda ake kai wa kai tsaye a kan irin wadannan wuraren da kuma kan ma'aikatan lafiya da kan malaman makaranta, za su iya zama laifukan yaki.

Unicef ta yi kira ga kasashen duniya da su bayar da goyon baya don samar da makarantun da za a samar da kwanciyar hankali.